News
Babban bankin Najeriya CBN ya umarci bankuna su tura kudaden asusun da suka daina aiki
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Babban bankin Najeriya CBN ya umarci bankuna da su tura kudaden suka rage cikin asusun bankunan da suka lalace ko aka daina amfani dasu ga wani asusu da ya samar.
PRNIGERIAN ta ruwaito cewa Wannan umarni na cikin wata sanarwar manema labarai da bankin ya fitar ranar juma’a mai dauke da sa hannun daraktan dake kula da sashen kudi da daidai tsare tsaren bankuna john Onojah.
Ta cikin sanarwa yace dukkanin kudin da masu su basu nema ba kuma suna cikin asusun da aka daina amfani da shi tsahon shekaru 10, za’a killace su a cikin asusun da ya samar mai suna Trust Fund Pool Account.
Daga bisa cbn yace da yuwuwar za’ayi amfani da kudin ne wajen saka jari da kuma inganta harkokin tsaron al’ummar kasar nan.
-
Opinion7 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion7 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News5 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
