News
Wasu Ɓatagari Sun Kwashe Wa Wani Dan Kasuwa Kuɗaɗe A Asusun Banki A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wasu ɓatagari da ba a san ko su wanene ba sun sace Kuɗaɗe asusun ajiyar bankin wani dan kasuwa mai Suna Alhaji Ibrahim Adamu, mai shekaru kimanin 55 mai sana’ar fasassun robobi da ledoji a Kasuwar ‘YanKaba dake jihar Kano.
Jaridar BIZ POINT ta ruwaito cewa Lamarin ya afku ne a jiya Talata, inda mutumin je ɗaya daga cikin bankunan da ke titin Murtala Muhammad a Kwaryar birnin Kano domin cire kuɗi.
Kwamishinan Yada Labarai Ya Gana Da Shuwagabannin Hukumomin Dake Karkashin Ma’aikatar Sa
A cewar sa, tun da fari ya cire Naira dubu 100 katin cirar kuɗi na ATM, in da ya sake yunƙurin cire Naira dubu 20, amma sai kuɗin ya ƙi fita, shi ne sai ya goge katin nashi a gashin kansa kamar yadda masu cirar kuɗi su ka saba yi idan kati ya ƙi cire kuɗi.
Ya na tsaka da goge katin sai wani mutum da ke tsaye a gefen shi ya ce “ Baba kawo in goge maka katin ka sake gwadawa”, sai kuwa ya miƙa masa katin, inda a nan ne ya ke zargin mutumin da ya nemi ha taimaka masa a she cutar sa ya yi.
Alhaji Adamu ya ƙara da cewa jim kaɗan bayan ya bar wajen cire kuɗin kawai sai ya ga saƙon kar ta kwana, wanda ke nuni da cewa an cire Naira dubu 500 da ga asusun na shi.
Hakan ta sa ya bazama izuwa bankin da asusun na shi ya ke domin shigar da korafi.
Ya kuma bayyana cewa a yanzu haka wadancan batagari sun samu nasarar kwashe kudi naira dubu 777 da ga asusun nasa.
Adamu ya ce, wancan mutumin da ya karbi katin cire kudi domin ya goge mishi ne ya sauya mishi da wani wanda ba na shi ba.
“Ban kuma gane cewa ya sauya mun katin na ATM ba sai da na je bankin su ka karba su ka duba a na’ura mai ƙwaƙwalwa, inda su ka sanar da ni cewa katin ba nawa bane, kuma a bankin ne ma aka gani cewa an kuma cire Naira dubu 200 da Kuma naira dubu 70 bayan an Fara cire Naira dubu 500.
“Da na sanar da bankin sun yi gaggawar toshe asusun tare da aikewa babban ofishin su korafin domin daukan matakin da ya dace”
Alhaji Adamu yayi kira ga Alumma da su gujewa fadawa hannun batagari tare da kiyaye Baiwa duk wani Wanda ba su sani ba katin cirar kudi da sunan zai taimaka musu.
“Duk kuma wanda yayi kokarin karbar katin cire kudi a hannun ka ka da ka bashi saboda cutar da kai zai yi kamar yanda aka yi mun,” in ji shi.
