News
Sabon Mai Baiwa Gwamnan Kano Ya Rasu Kwana Daya Bayan Rantsar Da Shi
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Sabon mai baiwa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf shawara kan aiyuka, Injiniya Ahmad Ishaq Bunkure ya rasu, kwana ɗaya da Gwamnan ya rantsar da shi a gidan gwamnati.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa da Jaridar INDA RANKA marigayin ya rasu a yau Laraba a kasar Egypt.
Wasu Ɓatagari Sun Kwashe Wa Wani Dan Kasuwa Kuɗaɗe A Asusun Banki A Kano
Sanarwar kara da cewa Gwamna Yusuf, wanda ya nuna kaɗuwa ga rasuwar Bunkure, ya baiyana mutuwar ta sa matsayin babban rashi ga iyalinsa da ma Kano baki ɗaya.
“Wannan wani yanayi ne na kaɗuwa da alhini saboda Injiniya Bunkure mutum ne mai hazaƙa da sanin makamar aiki wanda jihar Kano za ta amfani da shi.
” Allah Ya gafarta masa Ya baiwa iyalin sa da mu baki ɗaya hakurin rashin sa,” in ji Gwamnan.
