News
Bana Yin Shiri Da Shugaba Tinubu Saboda Yana Kawo Manufofin Da Suke Cutar Da Talakawa — Gwamnan Bauchi
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad, yace ba yayin shiri da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, saboda yana kawo manufofin da suke cutar da talakawan Najeriya.
Bala Mohammed Kauran Bauchi ya fa’dawa Sheikh Jingir hakan a lokacin wata Ziyara da shehun malamin ya Kai wa Gwamnan a gidan Gwamnatin Jihar dake Bauchi.
Sabon Mai Baiwa Gwamnan Kano Ya Rasu Kwana Daya Bayan Rantsar Da Shi
A Cikin wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumuntar zamani an Hango Gwamna Yana magana kan masu Muslim-Muslim Ticket tare da Halin da Gwamnatin ta jefa al’ummar Najeriya .
Bisa wasu kudure da Shugaban kasar ya gabatar musamman kudrin dokar sake Fasalin Harajin Wanda Gwamnan Yace Babu abinda dokar Zata haifar face cutar da Arewacin Nageriya .
Hakan yasa bana shiri da Shugaban kasa domin ya kawo tsarin da zai cutar da al’ummar Arewacin Nageriya inji Gwamna yake fadawa Sheikh sani Yahaya Jingir.
-
News5 days ago
Dakarun Soji Cafke Wani Shugaban ’Yan Ta’adda a Kaduna, Sun Kwato Harsasai 300
-
News6 days ago
Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar AP Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Dan-Shagamu
-
News19 hours ago
Rundunar ‘Yansanda Ta Yi Gargaɗi Gam Da Yiwuwar Kai Hare-hare Makarantu Da Wuraren Ibada
