Connect with us

News

Kwamitin Zaman Lafiya A Kano Ya Yi Allah Wadai Da Abinda Ya Faru Yayin Gudanar Da Zanga Zanga 

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Kwamitin zaman lafiya na jihar Kano yayi Allah Wadai da afkuwar munanan al’amura yayin gudanar da zanga-zanga.

Advertisement

Kwamitin ya bayyana hakan ne ta wani saƙon murya da shugaban sakatariyar (Amb. Ibrahim Waiya) ya fitar ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai Bashir A Bashir.

Cin Hanci Da Rashawa Shine Tushen Matsalar Najeriya – Masani.

Kwamitin zaman lafiyar ya bayyana takaicin sa duba da yadda matasa ke bada ƙofa ga wasu suna amfani dasu wajen lalata kadarorin gwamnati, da na ƴan kasuwanni da sunan siyasa. Amb. Waiya ya cigaba da cewa tun farko shugabannin zanga-zangar suna da laifi duba da yadda aka bayyana musu Abunda ka iya faruwa idan suka ce sai sun gabatar da wannan zanga-zanga amma sukai burus da wannan kiraye-kiraye suka fita sai gashi abunda suke hange ya afku.

Advertisement

Waiya ya kuma nuna takaicin sa bisa kwashe kayan ofishin hukumar Sadarwa ta ƙasa dake hanyar zuwa gidan gwamnati inda yace ba iya kanawa ne sukai asara ba har da jihohin arewa maso gabas, domin shine guri ɗaya tilo da Najeriya ta samar domin koyar da al’ummar arewa harkokin sadarwa.

A ƙarshe Waiya yaja hankalin masu haɗa wannan husuma inda ya tunatar dasu gobe ƙiyama domin rai zata girbi duk abinda ta shuka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending