News
Cin Hanci Da Rashawa Shine Tushen Matsalar Najeriya – Masani.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wani masanin tattalin arziƙi da ke jihar Kano ya bayyana cin hanci da rashawa a matsayin shine tushen matsalar Najeriya.
ABDULLAHI Tijjani , shugaban Responsive Citizens initiative ne ya bayyana hakan yayin Tattaunawa da Jaridar INDA RANKA a Kano
KANO: ‘Yan Sanda Sun Fara Bi Gida-Gida Suna Farautar Kayan Da Aka Wawushe Yayin Zanga-Zanga
“Matsalar hauhawar kayan masarufi yana da alaƙa da cire tallafin man Fetur da wutar lantarki da kuma rufe iyakokin ƙasar tare da cin hanci da rashawa, “in ji shi”.
Tijjani, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta karfafawa yan ƙasa gwiwa akan batun Noman Damuna, da na Rani domin kawo sauƙin kayan abinci.
A cewar sa, “Shugabanni ku zama masu kishin Ƙasa da kyawawan manufofi domin kyautatawa al’ummar Najeriya, “in ji Tijjani”.
Yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a fadin Najeriya.
