News
Ƴan Siyasa Na Haɗa Kai Da Ma’aikata Wajen Wawure Dukiyar Al’umma – Muhyi Magaji
DAGA YASIR KABIRU BASIRU
Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, ya bayyana yadda ƴan siyasa ke amfani da ma’aikatan gwamnati a jihar wajen wawure dukiyar al’umma.
Muhyi ya yi wannan furuci ne a wajen wani taron karawa juna sani na kwana ɗaya da hukumar ta shirya wanda ya sami haɗin gwiwar ofishin shugaban ma’aikatan jihar Kano da shirin ROLAC II na daraktocin ma’aikatan jihar kan yaƙi da cin hanci da rashawa kamar yanda WIKKI TIMES ta ruwaito.
Miji Da Mata Da ‘Ya’yansu Sun Mutu Sakamakon Cin Abinci Mai Guba
Shugaban, Ya bayyana cewa ya zuwa yanzu hukumar sa ta yi nasarar gano Naira Biliyan 18 da ake zargi ƴan siyasa tare da haɗin gwiwar wasu ma’aikatan Gwamnatin jihar Kano ne suka karkatar da su.
Ya ci gaba da cewa, “Ma’aikatan gwamnati suna da hannu dumu-dumi wajen almundahana a duk wasu shari’o’in da hukumar ta bincika don haka akwai bukatar a shirya taron karawa ma’aikatan gwamnati sani domin wayar musu da kai su daina yadda ƴan siyasa na amfani da su wajen aikata rashawa.”
“Kashi 90 cikin 100 na ayyukan cin hanci da rashawa ana yin su ne ta hanyar amfani da ma’aikatan Gwamnati.
“Muna da niyyar shirya shirin wayar da kan ma’aikatan gwamnati su daina yadda ƴan siyasa na amfani da su wajen karya doka”.
“An sha kama su suna aikata laifukan cin hanci, duk binciken da hukumar ke gudanarwa a Kano, yawanci ma’aikatan gwamnati su ne madogara a gudanar da su.”
