Connect with us

News

Kimanin Dalibai 503,275 Ne Suka Fadi Turanci Da Lissafi A Jarabawar WASSCE Ta 2024

Published

on

Da Ɗumi ƊumiWAEC ta Fitar Da Sakamakon Jarabawar WASSCE Ta 2024

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma WAEC ta ce kashi 73.79 cikin 100 na daukacin dalibai da  sun samu makin kiredit akalla darussa biyar masu dauke da harshen Ingilishi ko kuma lissafi.

Da yake magana a ranar Litinin da ta gabata ya yin da yake sanar da fitar da sakamakon jarabawar manyan makarantu na yammacin Afirka ta 2024, shugaban ofishin hukumar ta WAEC na Najeriya, Dokta Amos Dangut, ya ce WAEC ta hana sakamakon dalibai guda 215,267, wanda ya kai kashi 11.92 bisa 100 na ɗalibai guda 1,805,216, jimillar adadin na ‘yan takarar da suka rubata jarabawar.

Advertisement

Kimanin Dalibai 503,275 Ne Suka Fadi Turanci Da Lissafi A Jarabawar WASSCE Ta 2024

Jaridar INDA RANKA ta tuna cewa jarabawar 2024 ta dauki tsawon makonni bakwai da kwanaki shida kafin ta fito, daga ranar 30 ga watan Afrilu zuwa 24 ga watan Yuni, a fadin kasar.

Dangut ya ce ’dalibai guda 1,301,941, wadanda ke wakiltar kashi 72.12 cikin 100, sun samu kiredit  akalla darussa biyar da suka hada da Turanci da Lissafi.

Advertisement

Ya ci gaba da cewa, a cikin jimillar ‘ dalibai d a suka rubata jarabawar a Nijeriya, ‘yan takara guda 1,685,889, wadanda ke wakiltar kashi 93.39 cikin 100, an kammala tantance sakamakonsu gaba daya, ya yin da dalibai guda 119,327, wadanda ke wakiltar kashi 6.61 cikin 100, ke da daya ko fiye na darussan da suka yi ana sarrafa shi saboda wasu matsalolin da ake warwarewa.

Dangut ya kara da cewa WAEC ta hana sakamakon ɗalibai 215,267 wanda ya kai kashi 11.92 na ɗalibai guda 1,805,216, adadin wadanda suka zana jarabawar.

Advertisement

Ya ce ana ci gaba da rike sakamakon wasu rahotanni da aka samu na rashin gudanar da jarabawa.

Adadin sakamakon da aka hana a shekarar 2024 ya ragu da kashi 4.37 cikin 100 idan aka kwatanta da kashi 16.29 cikin 100 da aka rubuta na WASSCE ta ‘yan takarar shekarar 2023.

Advertisement

Ya ce, “Yawancin yin amfani da wayar salula a dakin jarabawar, duk da cewa an hana, da kuma yadda ake gudanar da magudi a wasu makarantu, wasu batutuwa ne masu ban tsoro.

“Ana binciken dukkan lamuran kuma za a gabatar da rahoton binciken ga kwamitin da ya dace na majalisar domin tantancewa da yanke hukunci na karshe.

Advertisement

 

“Za a sanar da hukunce-hukuncen kwamitin ga wadanda abin ya shafa ta makarantunsu daban-daban, nan gaba kadan. ’Yan takarar da wadannan shawarwarin suka shafa za su iya yin kira da a yi musu gyara idan sun ga dama ta shafin yanar gizon mu.”

Advertisement

Daga cikin dalibai guda 1,805,216 da suka rubata jarabawar a Najeriya, guda 896,894 sun kasance maza ne ya yin da guda 908,322 kuma mata ne, wanda ya nuna kashi 49.68 cikin 100 da kashi 50.32 bisa dari bi da bi.

An gudanar da jarabawar ta WAEC ne, a kasashe hudu da suka hada da: Najeriya, Gambia, Saliyo, da kuma Laberiya.

Advertisement

A wajen taron, Dangut ya koka kan yadda har yanzu majalisar take bin wasu jihohin basussuka, ya kuma kara da cewa ba za a fitar da sakamakon jarabawar jihohin da abin ya shafa ba har sai an biya su.

“Bai bukatar in sake bayyana cewa ba za a fitar da sakamakon ‘yan takarar da majalisar ta ke bin jihohin bashi ba a yanzu har sai an biya su.

Advertisement

“Muna kira ga wadanda abin ya shafa da su yi haka don bai wa makarantun da abin ya shafa damar samun sakamakonsu,” in ji shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending