Connect with us

News

Zan Lashe Zaben Shugaban Kasa Na Shekarar 2027. – Kwankwaso

Published

on

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dr Rabiu Kwankwaso

DAGA MUHAMMAD ZAHRADDIN TUKUNTAWA

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dr Rabiu Kwankwaso, ya bayyana cewa zai lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Advertisement

Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023, ya yi wannan furuci ne a ranar Asabar lokacin da ya kaddamar da sabuwar sakatariyar NNPP da ke kan titin IBB, Katsina.

Buncike Ya Gano Rashin Kwarewa Ne Ya Tilastawa Ajuri Ngilale Yin Murabis Daga Mukaminsa

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa ya ziyarci Katsina ne domin kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Yar’adua kan rasuwar mahaifiyarsu, Hajiya Dada.

Advertisement

A cewarsa, jam’iyyar ta shirya tsaf domin karbe shugabancin kasa, jihohi da sauran mukamai a fadin kasar nan a shekarar 2027.

Ya bayyana cewa jam’iyyar tana kan hanyar samun nasara a zaben shekarar 2027 sakamakon shirye da takeyi.

Advertisement

Shugaban Kwankwasiyya ya ce, “Ina so in tunatar da ku cewa jam’iyyar PDP ta riga ta mutu, saboda mun kasance a jam’iyyar, tun da suka kauce hanya, muka yanke shawarar ficewa.”

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya, musamman mata da matasa, da kada su bari a yaudare su da taliya, shinkafa ko kudi a lokacin zabe na gaba.

Advertisement

Kwankwaso ya kuma yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su kara jajircewa wajen ganin an samu nasarar jam’iyyar a jihar da kuma kasa baki daya.

Ya yaba musu da sauran masu ruwa da tsaki a jihar kan gyaran sakatariyar jihar, yana mai cewa hakan wani bangare ne na shiri don samun nasara.

Advertisement

Shugaban NNPP ya kuma yi alkawarin tallafa wa wani karamin yaro mai suna Abubakar Ibrahim daga unguwar Yammawa da ke fama da cutar tamowa.

Shi ma da yake jawabi, shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Armaya’u Abdulkadir, ya ce jam’iyyar na yin duk mai yiwuwa wajen wayar da kan masu zabe kan sabon tambarin jam’iyyar.

Advertisement

A cewarsa, sabon tambarin na nufin ilimi ga kowa da kowa, wanda shi ne babban abin da shugaban Kwankwasiyya ya fi damuwa da shi.

Ya ce, “Akwai bukatar jam’iyyar ta fara gangamin wayar da kan al’ummar karkara domin sanar da mambobi muhimmancin sabon tambarin.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending