Connect with us

News

Akalla Mutane 350 Suka Kamu Da Cutar Daji A Jihar Katsina

Published

on

Sama da mutane 350 suka kamu da cutar Daji a Katsina

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Akalla mutane 350 suka kamu da cutar Daji a karamar hukumar Batsari dake jihar  Katsina

Advertisement

Ɗan majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Batsari Hon.Mustapha Tukur Ruma ya bayyana haka a zauren Majalisar dokoki na Katsina kamar yanda jaridar BLUEPRINT ta ruwaito.

Kotu Ta Sanya Ranar Da Za Ta Yanke Hukunci Kan Rikicin Masarautar Nassarawa

Yayi kira ga Majilisar da ta buƙaci gwamnatin jihar da ɗauki matakin gaggawa akan ɓullar cutar Daji a ƙaramar hukumar kada ta bazu a sauran ƙananan hukumomin da suke maƙwabtaka da mazaɓar sa.

Advertisement

Ɗan Majilisar yace,”akwai halin matsi na rayuwa ga kuma wannan annoba ta cutar Daji,idan kaje asibiti zaka ga masu ɗauke da cutar suke ciki”.

Bayan tattaunawa akan ƙudirin kakakin majalisar Rt Hon Nasiru Yahaya ya buƙaci akawun majalisar daya turawa ɓangaren zartarwa domin ɗaukan mataki cikin gaggawa.

Advertisement

Ɗaukacin yan majalisar sun amince da a hanzarta aikawa gwamnatin jihar da ta ɗauki matakin gaggawa domin ceto rayukan al’ummar yankin daga wannan cutar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending