Connect with us

News

Kwankwaso Kwararre Ne Wajen Iya Jagorancin Al’umma —Saraki 

Published

on

Kwankwaso kwararre ne wajen iya jagoranci Saraki 
https://indaranka.com/2024/10/21/kwankwaso-kwarar…jagoranci-saraki/

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Tsohon shugaban majalisar dattawa ta ƙasa, Dr. Abubakar Bukola Saraki, ya ce tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kwararre ne wajen iya jagoranci.

Advertisement

Saraki ya bayyana haka ne a saƙon taya Kwankwaso murnar cika shekara 68 da haihuwa a yau 21-10-2020.

Jami’an Hukumar NDLEA Sun Samu Nasarar Gano Muggan Kwayoyi A Gidan Wani Sanata

A cikin wata sanarwa da mataimakinsa a kan kafafen yada labarai, Abba Gwale ya fitar, Saraki, ya bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan uwa kuma aboki wanda kuma ya kware wajen iya jagoranci.

Advertisement

“Abokina kuma ɗan uwana, tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kasance ƙwararren ɗan siyasa kuma jagora na gari.

“A yau da yake murnar zagayowar ranar haihuwarsa, ina taya iyalansa da ƴan uwansa da mabiyansa murnar wannan rana, sannan ina roƙon Allah ya ci gaba da ƙarfafa masa gwiwa, ya bashi cikakkiyar lafiya da basira da tsawon rai”. Inji Saraki.

Advertisement

Saraki da Kwankwaso dai sun yi aiki tare a majalisa ta takwas, a lokacin da Sarakin, wanda shima tsohon gwamnan jihar Kwara ne, yake matsayin shugaban majalisar dattawa daga shekara ta 2015 zuwa 2019, lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending