Connect with us

News

Jami’an Yan Sanda Sun Kama Wata Mata Mai Shekaru 54 Da Alburusai 350

Published

on

Yan Sanda Sun Kama Wata Mata Mai Shekaru 54 Da Alburusai 350

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Jami’an ‘yan sanda  sunyi nasarar kama wata Mata, Hamsatu Modu, mai shekaru 54, da alburusai guda 350 a jihar Yobe

Advertisement

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, ya fitar.

Kwankwaso Kwararre Ne Wajen Iya Jagorancin Al’umma —Saraki 

A cewar sanarwar, Matar da aka kama ‘yar asalin wani kauye ne mai suna Jakana da ke karkashin karamar hukumar Konduga ta Jihar Borno.

Advertisement

A cewar DSP Dungus, jami’an rundunar ‘yan sanda na ofishinsu, ‘A’ Divisional Police Headquarters, da ke garin Damaturu sune suka samu nasarar kama matar.

A cewar sa, tun da farko, rundunar ‘yan sanda ta samu rahoton sirri da ya tabbatar da cewa akwai wani mai safarar makamai yana hanyar shigowa Damaturu.

Advertisement

“Bamu bata lokaci ba wajen saka shinge a kan hanya Wanda ya bamu damar tsare wata mota kirar Golf 3 inda muka gano alburusai 350 a boye a cikin jakar kayan wacce muke zargi.

“Yanzu haka wacce mu ka kama tana fuskantar tuhuma tare da bincike domin gano wadanda ta ke aiki tare da su da kuma manufar safarar alburusan da mu ka kama a tare da ita,” a cewar DSP Dungus.

Advertisement

Ya Kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan Yobe, Garba Ahmed, ya jaddada kudirin jami’ansa na cigaba da aiki tukuru domin kawo karshen aiyukan ta’addanci a sassan jihar.

Kazalika, ya bukaci mazauna jihar Yobe su cigaba da bawa rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro goyon baya a yunkurinsu na tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending