Connect with us

News

Ƙuncin rayuwar da ƴan Najeriya suke ciki a yanzu akwai laifin tsofaffin shugabannin Ƙasa – Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam 

Published

on

IMG 20241022 WA0002

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Ƙungiyar wayar da kan jama’a da kare haƙƙin ɗan adam da tallafawa mabuƙata ta Awareness for Human Right and Charity Foundation, ta ƙalubalanci tsofaffin shugabannin Najeriya, kan yadda ta zarge su da gaza taɓuka abin a yaba wajen zama da gwamnatin tarayya domin lalubo hanyoyin magance tsadar rayuwar da yake damun al’umma a ƙasar.

Daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Auwal Usman Awareness shi ne ya bayyana hakan yayin zanatawar da da manema labarai a ranar Asabar 19 ga watan Oktoban 2024.

Advertisement

Jami’an Yan Sanda Sun Kama Wata Mata Mai Shekaru 54 Da Alburusai 350

Awareness ya ce duba da yadda al’ummar Najeriya ke ci gaba da fuskantar halin matsin rayuwa, da ta matsalar tsaro akwai buƙatar tsofaffin shugabannin, irin su Olusegun Obasanjo, da Abdulsalam Abubakar, da sauransu su yi zama na musamman da shugaba Tunibu, domin lalubo bakin zare kan magance matsalolin da ke damun al’umma.

 

Advertisement

Kwamared Auwal ya kuma yi kira ga shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tunibu da ya gaggauta samar da hanyoyin magance matsalolin tsaron, da ta ƙuncin rayuwa domin ganin al’ummar Ƙasa sun samu wani sauƙi.

 

Advertisement

“Yanzu haka ta kai ga mutane suna mutuwa, yara suna gujewa zuwa makaranta, aure na mutuwa, ƴan Ƙasa na kwana a kan hanya da kuma bin layuka, suna kuma talakawa ƙasashen ketare zuwa neman kuɗi, dukka saboda tsananin rayuwar da ke damun su a Najeriya, “in ji Auwal”.

 

Advertisement

Jaridar Indaranka ta rawaito cewa wannan dai na zuwa ne bayan da al’ummar Najeriya ke ci gaba da neman ɗaukin mahukunta ka halin ƙuncin rayuwar da suka samu kan su yanzu a ciki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending