Connect with us

News

Jami’an Hukumar NDLEA Sun Samu Nasarar Gano Muggan Kwayoyi A Gidan Wani Sanata

Published

on

Jami'an Hukumar NDLEA Sun Samu Nasarar Gano Muggan Kwayoyi A Gidan Wani Sanata
Shugaban hukumar Burgediya Janar Muhammad Buba Marwa,

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta samu nasarar gano muggan kwayoyi masu bugarwa a gidan Sanata Oyelola Yisa Ashiru, na jam’iyyar APC, mai wakiltar kudancin jihar Kwara.

Advertisement

Shugaban hukumar Burgediya Janar Muhammad Buba Marwa, ne ya sanar da hakan a yau lokacin da yake jawabi ga manema labarai.

Kafa Jami’ar Northwest Da Wudil Sune Mafi Kyawun Nasarorin Da Na Samu A Matsayin Gwamna — Kwankwaso

Ya ce jami’an hukumar NDLEA ne suka mamaye gidan Sanatan dake birnin Ilorin tare da binciko kwayoyin.

Advertisement

Mai magana da yawun hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ne ya sanar da hakan a yayin gabatar da jawabin a madadin Buba Marwa, inda yace an kama masu taimakawa Sanatan su uku sannan aka gurfanar da su har an yankewa daya hukuncin zaman gidan gyaran hali a watan Yuni na wannan shekara.

Babafemi, ya kalubalanci kalaman Sanata Oyelola, da ya ayyana hukumar NDLEA da cewa tana aiwatar da cin hanci da rashawa a ayyukan ta.

Advertisement

A kwanakin baya jaridar Daily Trust, ta rawaito labarin da Sanata Oyelola, yake cewa hukumar NDLEA ce babbar hukumar gwamnati mai aiwatar da cin hanci da rashawa a fadin Nigeria

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending