Connect with us

News

Kafa Jami’ar Northwest Da Wudil Sune Mafi Kyawun Nasarorin Da Na Samu A Matsayin Gwamna — Kwankwaso

Published

on

Kafa Jami’ar Northwest Da Wudil Sune Mafi Kyawun Nasarorin Da Na Samu A Matsayin Gwamna Kwankwaso

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa kafa jami’ar Northwest da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil sune mafi kyawun nasarorin da na samu tsawon wa’adi biyu da ya yi yana mulkin jihar.

Advertisement

Kwankwaso, shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, ya bayyana haka, a wajen kaddamar da wani shirin horas da malamai da nufin bunkasa ilimin kwamfuta na malaman firamare da sakandare 1,000, tare da hadin gwiwar jami’ar Skyline ta Najeriya da ke Kano a ranar Litinin.

Hedkwatar Tsaron Najeriya Ta Ce Babu Wanda Aka Naɗa A Matsayin Muƙaddashin Janar Lagbaja

Taron dai na daga cikin bukukuwan cikar sa shekaru 68 da haihuwa.

Advertisement

A cewar Kwankwaso, a shekaru biyu da ya yi a shekarar 1999 da 2012, ya aiwatar da ayyukan raya kasa da dama da suka hada da noma, samar da ababen more rayuwa, da raya karkara, da dai sauransu amma kafa jami’o’in biyu ya fi daraja a gare shi.

A cewar Kwankwaso, Gwamna Yusuf ya cancanci yabo domin ya kiyaye akidar tafiyar Kwankwasiyya, wato ilimi da ci gaban dan Adam

Advertisement

A nasa jawabin, gwamna Yusuf ya yaba da shirin horar da malamai 1,000 kan ilimin kwamfuta tare da hadin gwiwar jami’a mai zaman kanta

Yusuf ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kai da jami’o’i masu zaman kansu wajen horar da malamai da kuma kara kwazo domin samun nagartar ilimi a jiha

Advertisement

Ya yabawa Kwankwaso a matsayin jagora kuma jagoransa, inda ya yi alkawarin ci gaba da bin tsarin tafiyar Kwankwasiyya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending