Connect with us

News

Ci Gaba Da Hakuri Khalifah Muhammad Sanusi II

Published

on

download (1)

 

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Advertisement

 

Assalamu alaikum

Advertisement

 

Allahu Akbar! Ci gaba da hakuri, ci gaba da tsayuwa da kafarka ya Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Dr. Muhammad Sanusi II. Kaci gaba da ayukkan alkhairi da ka saba gudanarwa a koda yaushe. Kar kaji tsoron kowa sai Allah. Kar kayi shakkar kowa. Kar wanda ya baka tsoro. Babu wanda zai iya ganin bayan ka wallahi. Lallai Allah Subhanahu wa Ta’ala ya tara maka dimbin makiya saboda daukaka da daraja da yayi maka, domin su zama jarabawa a gare ka. Amma da ikon Allah babu ranar da zasu ci nasara akan ka. Saboda addu’ar iyaye, da addu’ar Malamai, da addu’ar masoya, da addu’ar bayin Allah da kuke taimakawa a koda yaushe. Kar ka damu, duk hasadar mahassada ba komai bace akan ka illa tamkar takin zamani da ake zubawa shuka. Haka zasu ci gaba da ganin ka Bi’iznillah. Bakin ciki ne zai zama sanadiyyar halakar su da ikon Allah. Allah Subhanahu wa Ta’ala yana tare da kai har kullun, kuma a koda yaushe. Kullun burin su shine, su ga sun tozarta ka, amma Allah Subhanahu wa Ta’ala yaki yarda da hakan. Maimakon tozarta, kullun kara daukaka kake yi. Maimakon su ga kayi kasa, kullun sai kara sama kake yi. Ba wani abu ne ya jawo hasadar da suke yi maka ba illa suturar da Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi maka. Shekara da shekaru suna yakar ka, amma Allah ya hana su cimma burin su. Suna yi maka sharri, suna yi maka karya, suna yi maka kage, suna bin ka da makirci kala-kala, iri-iri. Suna yi maka bita-da-kulli, suna cin dunduniyar ka, basu so su san alkhairin ka, suna bincike akan kuskuren ka domin su yada, amma Allah yaki basu damar da suke son samu akan ka. Idan kayi magana, sun san manufar ta, kuma sun san me kake nufi, amma sai su canza ta da gangan. Sun bi duk wani lungu, da duk wani sako, da duk wani kwararo domin samun damar tadiye ka, amma Allah yace hakan ba zai yiwu ba. A koda yaushe, a kullun suna kashe makudan kudade, suna kashe dimbin dukiya, domin kokarin ganin bayan ka, amma Allah yaki yarda da zaluncin su. Suna bin ka da sharri, kai kuma kullun kana bin su da alkhairi. Sun yi kokarin bata tsakanin ka da gwamnatota, da ‘yan siyasa, da sarakuna, da Malamai, da talakawa, da masu kudi, da ‘yan kasuwa, amma dai har yanzu sun kasa cimma nasara. Kai hatta matsayin da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya baka na Khalifancin darikar Tijjaniyyah, ba tare da kai ne ka nema ba, shi ma kullun damun su yake yi. Don haka kaci gaba da hakuri, domin babu abunda hakuri zai kara maka illa daukaka da daraja. Suna bin duk wasu hanyoyi na tsibbace-tsibbace, da sihirce-sihirce, da tsafe-tsafe, da bokanci, da harkar bori, domin su ga sun kai ka kasa, amma basu san kai Allah ne ka rike ba, alhali sun manta, duk wanda yake rike da Allah, to wallahi babu wani mahaluki da zai iya ganin bayan sa. Ka bar su da shirmen su suyi tayi, kai dai ci gaba da rike Allah Subhanahu wa Ta’ala!!!

Advertisement

 

Wassalamu alaikum,

Advertisement

 

Imam Murtadha Muhammad Gusau. 08038289761, 26/11/2024.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending