News
Yan Daba Sun Kashe Abokin Ango A Taron Ɗaurin Aure
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI
’Yan daba sun kashe wani ɗan shekara 25 a wurin taron ɗaurin auren babban abokinsa a Jihar Neja.
Matashin, mai suna Murtala Hassan, wanda shi ne babban abokin ango ya gamu da ajalinsa ne a yayin da yake rabon faɗa a wurin bikin auren a unguwar Barkin-Sale da ke garin Minna.
Mun Kama Masu Kwacen Wayoyi 1372, Da Masu Fadan Daba Sama Da 3000 — Anti Snatching Force
Shaidu sun ce matashin wanda ke sana’ar ɗinki ya rasu ne bayan an soka masa wuƙa a rikicin ƙungiyoyin ’yan daba masu gaba da juna ranar Lahadi da misalin ƙarfe 10 na dare.
Wani mazaunin unguwar Barikin-Sale ya ce, rikicin kungiyoyin an daɗe ana yin sa, ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
Kakakin ’yan sanda a Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa sun samu rahoton kashe matashin a lokacin da yake ƙoƙarin raba faɗan ɓata-gari.
Ya ce ’yan sanda sun je sun ɗauke gawar a wurin inda suka kama mutum guda da ake zargi, amma ana ci gaba da bincike domin gano gaskiyar lamarin kamar yanda Jaridar AMINIYA ta ruwaito
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
