Connect with us

News

Sarkin WASE Ya Gaura Wa Waziri Tafi A Fada

Published

on

images (3)

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Sarkin WASE Alhaji Muhammadu Sambo Haruna ya lakadawa wazirin sa Alhaji Muhammadu Badamasi shegen duka ana tsaka da fadanci a fadar masarautar dake Wase jihar Filato.

Advertisement

A rahoton da jaridar Daily Trust ta ruwaito an ji cewar,dalilin faruwar wannan mari ya samo asali ne sakamakon wani aiki da Sarkin ya sa Waziri shikuma ya yi biris ya ki aikatawa wanda hakan ne ya harzuka sarkin.

Gwamna Na Shirin Sayar Da Man Fetur A Jihar Sa Kan N600 Duk Lita

Duk da dai dama akwai tsohuwar tsama tsakanin Sarkin da Waziri, wanda har yanzu aka kasa samun jituwa.

Advertisement

Majiyoyi sun labarto cewa a makon daya gabata ne aka ji sarkin na tambayan wazirin dalilin rashin aiwatar da ayyukan sa yadda ya kamata inda shi kuma wazirin ya mayar da martani cikin zafi. Faruwar hakan ya fusata sarkin wanda ta kai ga ya mike daga karagarsa ya dumfari Wazirin na sa,Ko da isan sarkin gaban waziri a nan ne lamari ya muzanta duka ya shiga tsakani.

A nasa bangaren bayan faruwar lamarin sarkin nan yakai kara zuwa ofishin ‘yan sanda

Advertisement

Sai dai yan sanda basu sami damar kama wazirin ba domin ya bayyana musu cewa al’ada tayi hanin kamen basarake da dare amma ya yi alkawarin kai kansa ofishin ‘yan sanda washe gari.

Haka kuma Majiyoyin ‘yan sanda da ke Jos sun tabbatar da cewa an gama bincike tsaf kuma an mika shariar zuwa kotu. Duk da , ba a samu damar jin ta bakin mai magana da yawun fadar ba, haka zalika jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, DSP Alabo Alfred, har yanzu shima baice komai ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending