News
Jami’an Hukumar EFCC Sun Kama Ma’aikatan Haraji 5 Bisa Zargin Wawure Naira Biliyan 1.2 A Katsina
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kama ma’aikatan haraji a jihar Katsina bisa zargin zambar kudi naira biliyan N1,294,337,676.53 da suka shigo wa jihar daga hukumar lafiya ta duniya da sauran wasu hukumomin daga ketare.
Wadanda ake zargin sun hada da Rabiu Abdullahi, Sanusi Mohammed Yaro, Ibrahim M. Kofar Soro, Ibrahim Aliyu da Nura Lawal Kofar Sauri.
An kama su ne biyo bayan wani koke da gwamnatin jihar Katsina ta shigar na cewa wadanda ake zargin sun hada baki tare da karkatar da kudaden da suka kai N1,294,337,676.53 daga hannun hukumar lafiya ta duniya.
Binciken da hukumar ta yi ya nuna cewa Nura Lawal da kamfanin sa na ”NADIKKO” da su ake amfani wajen karkatar da kudaden da aka wawure,wadannan kudade da aka wawure an gano su ne a asusun bankuna daban daban na wadanda ake zargin.
Yanzu haka dai wadanda ake zargin suna tsare a ofishin hukumar EFCC shiyyar Kano kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.
