News
Gwamnatin Tarayya Ta Karyata Jita-jitar Karin Farashin Wutar Lantarki
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta karyata labarin da ke yawo cewa tana shirin ƙara farashin wutar lantarki nan da wani lokaci kaɗan.
Mai ba Shugaban Kasa shawara a harkokin makamashi, Olu Arowolo, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta jaddada cewa an fassara kalamanta ba daidai ba, wanda ya haifar da rahotannin da ke cewa za a yi karin kudin wuta da kashi 65 cikin 100.
Yan Bindiga 23 Sun Ajiye Makamansu Bayan Wani Musayar Wuta Tsakaninsu Da Sojoji
Wasu kafafen yaɗa labarai sun ruwaito cewa Olu Arowolo ta yi wannan furuci ne a taron makamashi na Afirka da aka gudanar a birnin Dar es Salaam, kasar Tanzaniya. Sai dai ta bayyana cewa manufar bayaninta ita ce bayan an yi karin kuɗin wutar lantarki na Band A a shekarar 2024, a halin yanzu kuɗin da ake samu daga masu amfani da wutar lantarki yana biyan kashi 65 cikin 100 na kuɗin samar da ita, yayin da gwamnatin tarayya ke cigaba da biyan giɓin da ake samu.
Ta kuma nanata cewa babban burin gwamnatin tarayya shi ne inganta fannin samar da wutar lantarki da kuma magance matsalolin da suka shafi durƙushewar babbar hanyar rarraba wutar lantarki a ƙasar.
Gwamnati na ci gaba da jajircewa wajen ganin an samu ingantacciyar wutar lantarki ga ‘yan Najeriya, tare da rage dogaro da tallafin da ke haifar da gibin kuɗi a fannin samar da makamashi.
