News
Zan Iya Rantsuwa Da Al’Kur’ani Aisha Binani Ce Ta Lashe Zaben Adamawa Ba Fintiri Ba — Kwamishinan Zabe Hudu Ari
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Tsohon Kwamishinan Hukumar Zabe da ya ayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben Gwamnatin Adamawa , Barista Hudu Ari ya ce bazai taba yin nadama ko Kuma karyata sakamako akan cewar ba ita bace ta lashe zaben a zaben shekarar 2023 ba.
Hudu ya ce tabbas bazai taba janye kalamansaba wai dan majalisar tarayya ta amince da korar sa a matsayin wanda ya bayyana gaskiya
Cikin wani taron manema labarai da yayi a Bauchi, ya yi rantsuwa da Alkur’ani cewa yana da shaidun da za su tabbatar da cewa Aisha Binani ta kayar da gwamnati mai ci ta Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP.
An dai dakatar da Barista Hudu Ari ne saboda ya ayyana Binani a matsayin wadda ta ci zabe ana tsaka da kirga kuri’u.
Idan za’a iya tunawa dai barista Audu Ari shine ya fara fitar da sakamakon zaben Jihar Adamawa inda ya ayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben da kiri’u masu rinjaye
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
