Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Kara Shekarun Ritayar Jami’an Lafiya Domin Hana Ficewarsu Kasashen Waje

Published

on

doctors (1)

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnatin Tarayya ta sanar da karin shekarun ritaya ga jami’an lafiya daga shekaru 60 zuwa 65 a kokarinta na rage matsalar ficewar kwararrun ma’aikata zuwa kasashen waje.

Advertisement

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya amince da wannan sabon mataki domin karfafa bangaren kiwon lafiya a Najeriya.

Rundunar ‘Yan Sandan Bauchi Ta Kama Wata Mata Bisa Zargin Kashe Kishiyarta

Wannan mataki na zuwa ne bayan rahotannin da suka nuna cewa fiye da kashi 50% na kwararrun jami’an lafiya sun bar kasar cikin shekaru goma da suka gabata, kamar yadda binciken da kungiyar Likitocin Najeriya (NMA) ta bayyana.

Advertisement

Mataimakin shugaban NMA, Benjamin Olowojebutu, ya ce karin albashi, horo da damar ci gaba da karatu na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen rage yawan ficewar kwararrun jami’an lafiya daga Najeriya.

Gwamnati na fatan wannan sabon mataki zai taimaka wajen bunkasa bangaren kiwon lafiya da kuma inganta jin dadin ma’aikatan lafiya a kasa.

Advertisement

 

 

Advertisement

PREMIUM TIMES

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending