Connect with us

News

Mahaifin Dan Bijilanti Da Aka Kashe A Tawagar Sarkin Kano Ya Bukaci Adalci Da Diyya

Published

on

WhatsApp Image 2025 04 01 at 20.19.06 1 1

Mahaifin Surajo Rabiu, daya daga cikin ‘yan bijilanti na unguwar Jaba a karamar hukumar Fagge, Jihar Kano, ya bukaci a bi masa hakkin dansa tare da biyan diyya bayan kisan da aka yi masa a cikin tawagar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, bayan sallar Idi.

A wata tattaunawa da jaridar SOLACEBASE, mahaifin mamacin, Muhammadu Rabiu, ya bayyana yadda lamarin ya faru har ya kai ga mutuwar dansa. Ya ce Surajo ya fara yanke shawarar kin halartar sallar Idi, inda ya ci gaba da aikin gyaran na’urorin lantarki. Amma daga bisani ya canja ra’ayi, ya sanya kayan aikinsa na bijilanti, sannan ya fita zuwa wurin sallar .

Advertisement

CBN Ya Musanta Samar Da Sabbin Takardun Kudin N5,000 Da N10,000

Surajo, mai shekaru 26, shi ne na hudu a cikin ‘ya’yan Muhammadu Rabiu goma sha biyu. Mahaifinsa ya bayyana marigayin a matsayin matashi mai biyayya da hakuri. “Dansu ya sadaukar da kansa don tsaron al’umma,” in ji shi. “Yana aiki ne a matsayin mai tsaro don kare rayuka da dukiyoyi, amma aka kashe shi yana bakin aiki.”

Mahaifin marigayin ya bukaci gwamnatin Jihar Kano da Masarautar Kano da su tabbatar da gudanar da bincike mai adalci domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da biyan diyya ga iyalansa.

Advertisement

“Surajo matashi ne mai tarbiyya da mutunci. Bai taba shan taba ba, balle ya yi hulda da mugayen mutane. Makwabtanmu za su iya tabbatar da hakan,” in ji mahaifin marigayin.

Bayan wannan mummunan hari da aka kai wa ‘yan bijilanti a tawagar Sarkin Kano a ranar Lahadi, 30 ga watan Maris, jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da cewa har yanzu ana ci gaba da bincike. A halin yanzu, Muhammadu Rabiu tare da shugabannin kungiyar ‘yan bijilanti suna kokarin ganin an yi adalci kan kisan Surajo.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending