News
Tsohon Alkalin Babban Kotun Kano, Mai Shari’a Wada Umar Rano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 75
Tsohon alkalin Babban Kotun Jihar Kano, Mai Shari’a Wada Umar Rano, ya rasu yana da shekaru 75 a duniya, bayan fama da jinya mai tsawo.
Marigayin ya rasu ne da safiyar yau Alhamis a wani asibiti da ke cikin birnin Kano. Ya yi ritaya daga aikin shari’a a shekarar 2014, bayan shekaru da dama na hidimar gaskiya da rikon amana a cikin kotunan jihar Kano.
Mai Shari’a Rano ya shahara da jajircewa da kishin gaskiya, inda ya taka rawar gani a fagen shari’a da kuma hidimar jama’a. Daya daga cikin muhimman ayyukansa na ƙarshe shi ne jagorantar Kwamitin Binciken Batan Yara a jihar Kano – lamari da ya jawo hankalin al’umma a lokacin mulkin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Ya bar mata biyu, da ‘ya’ya da jikoki da dama.
Advertisements
