Connect with us

News

Fursunoni 62 Sun Kammala Karatun Sakandare A Gidan Gyaran Hali Na Kano

Published

on

FB IMG 1744933726977

Fursunoni 62 da ke zaune a Gidajen Ajiya da Gyaran Hali a jihar Kano sun kammala karatun sakandare, tare da samun horo na musamman a fannin karatun Al-Qur’ani mai girma.

Wannan ci gaba na zuwa ne sakamakon kokarin gwamnatin jihar Kano na farfado da harkar ilimi, wanda ya hada har da fursunonin da ke cikin gidan gyaran hali. A cewar Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, gwamnati ta riga ta ayyana dokar ta baci kan ilimi domin shawo kan matsalolin da suka dabaibaye fannin ilimi a jihar.

Advertisement

Za a Kashe Ɓeraye A Garun Malam Domin Hana Yaduwar Cutar Lassa – Gwamnatin Kano

Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali a Kano, Alhaji Ado Inuwa, ya bayyana farin cikinsa da irin gudunmuwar da gwamnatin jihar ke bayarwa wajen inganta rayuwar fursunoni, musamman a bangarorin lafiya da ilimi.

Shi ma DCC Mu’azu Tukur (mai ritaya) ya bayyana cewa shirin karatun hadin gwiwa ne tsakanin Gidan Gyaran Hali da Makarantar Sakandaren Koyon Harshen Larabci ta Kano (S.A.S), da kuma Hukumar Ilimin Sakandare ta K.E.R.D.

Advertisement

Taron bikin kammala karatun ya samu halartar wakilai daga sassa daban-daban na jihar, lamarin da ke nuna yadda al’umma ke ci gaba da fahimtar muhimmancin ilimi ga kowane bangare na rayuwa, ciki har da fursunoni.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending