Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Shirya Bita Ga Limaman Juma’a Don Karfafa Huldar Al’umma Da Gwamnati

Published

on

IMG 20250429 WA0072

A wani sabon mataki na karfafa zumunci da fahimta tsakanin gwamnati da al’umma, Gwamnatin Jihar Kano ta shirya taron karawa juna sani na kwanaki biyu ga Limaman masallatan Juma’a daga sassa daban-daban na jihar. Wannan bita na musamman na da nufin amfani da mimbari wajen yada sahihan bayanai da kuma karfafa zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’umma.

Da yake jawabi a lokacin bude taron, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa wannan shiri wani bangare ne na tsare-tsaren Gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na inganta hulda da shugabannin addini. Ya jaddada cewa gwamnati tana ganin malamai a matsayin ginshikan cigaban al’umma, kuma ba ta da wani ra’ayi na kaskantar da su.

Advertisement

An Rotsa Babura 601 A Abuja 601 A Abuja

Kwamishinan ya bukaci Limaman da su rika amfani da hudubobin Juma’a wajen isar da sakonni masu amfani, da ke gina kasa da nufin kawo ci gaba, da bayar da shawarar da za ta taimaki gwamnati wajen tafiyar da mulki bisa adalci da gaskiya.

 

Advertisement

A nasa bangaren, Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II, ya jaddada bukatar Limamai su mayar da hankali wajen koyar da zaman lafiya da hadin kai a cikin al’umma, maimakon kushe ko nuna bambancin akida, yana mai cewa mimbari na da matukar tasiri wajen gina kyakkyawar fahimta a tsakanin mutane.

Shugaban Majalisar Limaman Masallatan Juma’a na jihar, Sheikh Muhammad Nasir Adam, ya bayyana cewa shawara da suka shafi shugabanni za ta fi tasiri idan aka yi ta cikin sirri da mutunci. Ya yabawa gwamnati bisa wannan kira na tuntuba da hadin gwiwa.

Advertisement

Taron ya samu halartar daruruwan limamai daga dukkan kananan hukumomin jihar, inda aka tattauna hanyoyin inganta isar da sako ga al’umma cikin hikima da natsuwa, tare da manufar kyautata dangantaka tsakanin gwamnati da al’umma baki daya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending