Connect with us

News

Matar Aure Ta Kai Mijinta Kotu Saboda  Zargin Soyayya da Mage

Published

on

A ƙasar Indiya, wata mata ta kai ƙarar mijinta kotu bisa zargin yana ƙaunar mage fiye da ita – abin da ya tayar da hankali da dariya a lokaci guda.

Matar ta bayyana a gaban kotu cewa mijinta na nuna wa mage ɗin su kulawa ta musamman, yana shan wahalar barin mage ta damu, amma ita matar, ko kallon arziki bai cika yi mata ba.

Advertisement

Kotu Ta Yanke Wa ’Yan China Huɗu Hukuncin Zaman Gidan Kaso Na Shekaru Biyar

“Ina kwana da shi a gida, amma idan dare ya yi mu kwanta, sai mage ta zo ta dare kirjinsa ta kwanta kamar ita ce matar gidan. Idan na ce zan koreta, sai ta yawushe ni ko ta yi mini ihu. Shi kuma sai ya tsaya yana kallo kamar babu abin da ya faru,” in ji matar.

Bayan an saurari ƙarar, alkalin kotun ya fara zaton “Mage” wata mata ce da mijin ke hulɗa da ita a ɓoye. Sai dai bayan ya duba takardar ƙara da hoton mage a cikinta, ya fahimci magana ce ta mage na gaske – dabba.

Advertisement

Alkalin, cikin mamaki da dariya, ya ce, “Wannan ba ƙara ba ce, shirme ne da shashanci.” Ya yi watsi da ƙarar nan take.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta inda mutane ke tofa albarkacin bakinsu – wasu na cewa matar na da kishi fiye da kima, wasu kuma na ganin mijin bai yi adalci ba wajen nuna kulawa tsakanin abokiyar zama da dabbarsu.

Advertisement

 

 

Advertisement

INDIAN TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending