Connect with us

News

Sallah Ta Wuce Cikin Lafiya: Babu Cuta, Babu Damuwa – Cewar Gwamnatin Kano

Published

on

Abba

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana godiyarta ga al’ummar jihar bisa bin matakan kariya da Ma’aikatar Lafiya ta shimfida kafin bukukuwan Babbar Sallah domin kare lafiyar jama’a da ta dabbobin layya.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce bin wadannan matakai da suka hada da duba lafiyar dabbobi kafin yanka, tsaftace nama, da kuma dafa shi yadda ya kamata, ya taimaka wajen ganin an gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali da lafiya.

Advertisement

AKCCOSA 2021 Ta Shirya Babban Taron Sake Haduwa A Kano

Ya ce babu wani rahoton bullar cuta daga dabbobin layya ko abinci, wanda hakan ya nuna cewa matakan sun yi tasiri.

Dakta Yusuf ya jinjina wa jama’a bisa hadin kai da fahimta da suka nuna, yana mai cewa hakan ya kara tabbatar da yadda mutane ke fahimtar muhimmancin kiyaye lafiya.

Advertisement

Ya kara da cewa Gwamnatin Jihar Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta ci gaba da daukar matakai domin inganta kiwon lafiya da jin dadin al’umma.

A karshe, ya bukaci mutane da su ci gaba da kiyaye tsafta da bin shawarwari na lafiya a kowane lokaci domin kare kai da sauran jama’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending