News
AKCCOSA 2021 Ta Shirya Babban Taron Sake Haduwa A Kano
Kungiyar tsofaffin daliban Kwalejin Kasuwanci ta Al’umma da ke Kumbotso, Kano (AKCCOSA 2021), ta shirya babban taron sake haduwa domin karfafa zumunci da duba hanyoyin ci gaban makarantar da al’ummarta gaba daya.
Taron, wanda za a gudanar da shi a ranar Asabar, 14 ga Yuni, 2025 da misalin karfe 2:00 na rana, zai gudana ne a Dakin Taro na Maƙasudi da Dama (Multiple Purpose Hall) na makarantar AKCCC da ke Kano.
Jami’ar Northwest Ta Bai Wa Dalibai Damar Biyan Kuɗin Makaranta A Rarrabe
A cikin wata sanarwa da kwamitin shirya taron ya fitar, an bayyana cewa taron zai kasance dandali na tattaunawa, musayar ra’ayi da gina sabbin hanyoyin ci gaba ga tsofaffin dalibai da makarantar baki daya.
Wata majiya daga cikin kungiyar ta shaida wa wakilinmu cewa: “Mun shirya wannan taro ne domin hada kanmu da kuma tattauna makomar kungiyar da kuma yadda za mu tallafa wa almajirai da makarantar da ta raina mu.”
Ana sa ran halartar fitattun ‘yan kungiyar daga sassa daban-daban na kasa da ma waje, tare da fatan cewa za a yi amfani da wannan dama wajen hada kai da samar da mafita ga kalubalen da suke fuskanta a matsayinsu na tsofaffin dalibai da shugabannin al’umma.
Kungiyar ta bukaci kowa da kowa da ya tabbatar da halartarsa domin tabbatar da nasarar taron.
