Connect with us

News

Matasa Sun Fara Jan Ragamar Yaki da Wariya Ga Masu Bukata Ta Musamman A Kano

Published

on

IMG 20250624 WA0010

Wasu matasa a jihar Kano na karfafawa juna gwiwa wajen yakar wariya da nuna banbanci da ake wa masu larura, tare da kira ga gwamnati da ta dauki matakin da ya dace wajen kare hakkokin wannan rukuni.

Bashir Ali Haruna, matashi mai larurar kafa, ya bayyana yadda rashin tallafi daga gwamnati da wariya daga al’umma suka shafi rayuwarsa tun yana karami. Duk da kalubalen da ya fuskanta a lokacin karatun diploma, bai daina fatan gyara rayuwa ba.

Ƴan Sanda Sun Cafke Masu Satar Kayan Layin Dogo A Ilorin, Kano Da Gombe

“Na kammala diploma, amma na shafe lokaci ina neman aiki har sai da na samu damar shiga wani gidan rediyo mai zaman kansa,” in ji shi. Yanzu haka, Bashir ya koma karatu domin daukar darasi a matakin HND, yana mai cewa ilimi na daya daga cikin hanyoyin ficewa daga kangin wariya.

IMG 20250624 WA0008

Ya bukaci gwamnati da kungiyoyin farar hula da su samar da damammaki na ilimi da sana’o’i ga masu bukata ta musamman, yana mai cewa: “Karatu shi ne gatan mai bukata, kada kalubale su hana ci gaba.”

Kalubale da Warin Gaba

Rahotanni daga kungiyoyi masu zaman kansu sun nuna cewa masu larura a Najeriya na fama da matsaloli da suka shafi rashin damar samun ilimi, kiwon lafiya, sana’a da guraben aiki – dukkan wadannan abubuwa na daga cikin hakkokin dan Adam da doka ke karewa.

Advertisement

Yarima Sulaiman Ibrahim, shugaban wata kungiya da ke kare hakkin masu larura a Kano, ya ce shi ma yana fama da matsalar gani tun yana yaro.

“Da zarar mutum ya kamu da larura, ana jefar da shi daga harkokin rayuwa. Wannan dabi’a ce da ya kamata ta kare,” in ji shi.

IMG 20250624 WA0009

A cewarsa, akwai bukatar gwamnati ta daina daukar batun tallafa wa masu larura a matsayin taimako, yana mai cewa, “Ilimi, lafiya da sana’a ba taimako ba ne – hakkinsu ne.”

 

Dokar 2018 da Rashin Aiwarta

A shekarar 2018, gwamnatin tarayya ta amince da Dokar Kare Hakkin Masu Larura (Discrimination Against Persons with Disabilities (Prohibition) Act). Dokar na haramta nuna wariya da hana masu larura damammakin rayuwa.

Advertisement

Ta tanadi cewa dukkan matakan gwamnati – daga tarayya zuwa kananan hukumomi – su tabbatar da cewa gine-gine, makarantu, asibitoci da ababen sufuri sun dace da bukatun masu larura. Ana kuma bukatar daukar matakan da za su bai wa masu larura damar shiga rayuwar yau da kullum ba tare da tangarda ba.

An bai wa gwamnati wa’adin shekaru biyar daga 2019 zuwa 2024 domin tabbatar da dacewar muhallan jama’a da bukatun masu larura. Sai dai bayan cikar wannan wa’adi, masana da kungiyoyi na korafi cewa har yanzu ba a ga wani ci gaba mai gamsarwa ba.

Yunkurin Gwamnati: Daga Abuja zuwa Kano

A shekarar 2024, gwamnatin tarayya ta kara kasafin kudin Hukumar Kare Hakkin Masu Larura (NCPWD) da kaso 500 cikin 100, inda aka ware kusan naira biliyan 2.1 domin aiwatar da shirye-shiryen da suka hada da karfafa tattalin arzikin masu larura da inganta rayuwar mata masu nakasa.

A matakin jihar Kano, a cikin kasafin kudin 2024, gwamnati ta kara kudin Asusun Tallafa wa Masu Larura daga naira miliyan 100 a bara zuwa naira miliyan 197.3. Baya ga haka, an ware naira miliyan 158 domin shirye-shiryen horar da sana’o’i da wasu ayyuka na musamman.

Gwamnatin jihar na shirin kafa Hukumar Masu Bukata ta Musamman domin sa ido kan manufofin da suka shafi wannan rukuni na al’umma.

Advertisement

Bukatar Tsari da Wakilci

Dr. Nasir Yakubu Malami na Jami’ar Bayero, Kano, ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta tsara gine-gine da ababen more rayuwa da suka dace da nau’ukan larura, ciki har da makarantun gwamnati da kasuwanni da asibitoci.

Shi ma Dr. Binta Bala, daraktar ayyukan jin kai a jihar Kano, ta bayyana cewa matsala guda da ke hana ci gaba ita ce rashin wakilcin masu larura a cikin tsarin yanke shawara.

“Yawan lokacin da ake ba su mukamai na musamman ne kawai kamar SA ko PA, ba a basu cikakken dama a kujerun tsare-tsare,” ta ce.

Ta bukaci gwamnati da ta tabbatar da cewa ana hukunta duk wanda ya ci zarafin masu larura da gangan.

Kiran Matasa: Lokaci Ya Yi

Advertisement

Yayin da gwamnati ke cigaba da bayyana shirye-shirye, kungiyoyin matasa da masu fafutukar kare hakkin masu larura na bayyana cewa lokaci ya yi da al’umma za ta farka.

“Ba mu bukatar tausayi – muna bukatar adalci da kariya,” in ji Bashir Ali Haruna.

A cewarsu, masu bukata ta musamman ba za su cigaba da zama a gefe ba – sun fara daukar mataki da karfi da yaji, domin ganin cewa ana basu hakkinsu kamar kowane dan kasa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending