Connect with us

News

Hukumar Magunguna A Kano Ta Ce Ta Rage Bashin N1.2bn Da Ta Gada Daga Gwamnatin Baya

Published

on

Hukumar samar da magunguna da kayayyakin kula da lafiya ta jihar Kano ta ce ta rage kaso mafi yawan bashin da ta gada daga gwamnatin da ta gabata, inda ta ce yanzu saura naira miliyan 250 kacal daga cikin bashin naira biliyan 1.2.

Babban Daraktan hukumar, Pharmacist Ghali Sule, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron tunawa da cika shekaru biyu da jagorancinsa, wanda aka shirya domin haskaka manyan sauye-sauyen da aka samu karkashin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf a fannin lafiya.

Advertisement

Matashi Ya Nemi Shugabannin Najeriya Su Saurari Saƙonsa Kan Makomar Al’umma

A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Farouk Isa Musa, ya fitar, Darakta Ghali Sule ya ce hukumar za ta ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren gwamnati na yanzu tare da tabbatar da dorewar nasarorin da aka cimma.

Daga cikin sauye-sauyen da hukumar ta kawo akwai fara amfani da tsarin siyan magunguna ta kafar Intanet, wanda hukumar ta ce ya taimaka wajen rage kashe kuɗi, kawo sauƙi a lissafi da kuma tabbatar da gaskiya a cikin tsarin.

Advertisement

A nasa bangaren, Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Abubakar Labaran Yusuf, wanda Babban Sakataren ma’aikatar lafiya, Pharmacist Aminu Bashir, ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar ta zuba jari a gine-ginen masana’antun magunguna, ta kirkiri sabbin hanyoyin adanawa na zamani, tare da kafa dokokin da za su tabbatar da inganci a fannin lafiya.

Kwamishinan ya ce hakan na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin kyautata walwalar jama’a da tabbatar da samun magunguna cikin sauƙi da kuma a farashi mai rahusa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending