News
Yadda ‘Yan Bindiga Suka Sace Kansila Da Wasu Mutane A Katsina
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki garin Daudawa da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina, inda suka sace kansilan garin tare da wasu mutane da dama.
Lamarin ya faru ne da daren Talata yayin da maharan suka bayyana cikin makamai, suka fara harbe-harbe domin razana jama’a, kafin su yi awon gaba da mutanen da suka shirya sacewa.
Hukumar Magunguna A Kano Ta Ce Ta Rage Bashin N1.2bn Da Ta Gada Daga Gwamnatin Baya
Cikin waɗanda aka sace har da kansilan Daudawa, Honarabul Buhari Aliyu Daudawa, wanda ake cewa maharan sun tare shi ne a hanyarsa ta dawowa daga Funtua, kamar yadda wani mai sa ido kan sha’anin tsaro, Bakatsine, ya bayyana a shafinsa na X (tsohuwar Twitter).
“Mun fara jin karar harbe-harbe ne kawai. Kowa ya ruga cikin gida da gudu. Daga baya muka ji labarin an sace mutane, ciki har da kansilanmu,” in ji wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa.
Wata majiya ta ce maharan ba su shiga cikin garin Daudawa kai tsaye ba, sai dai sun tare hanya ne inda suka yi garkuwa da kansilan da wasu.
Faskari na daga cikin sassan Kudancin Jihar Katsina da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a kai a kai, duk da irin ƙoƙarin da hukumomin tsaro ke ci gaba da yi a yankin kamr yanda Jaridar WIKKI TIMES ta ruwaito
