Connect with us

News

Wani Saurayi Yayi Ajalin Budurwarsa Da Ke Shekarar Karshe A Jami’a

Published

on

Rundunar ƴan sandan Jihar Ondo ta tabbatar da kisan da aka yi wa wata ɗaliba da ke shekarar ƙarshe a Jami’ar Adekunle Ajasin da ke Akungba-Akoko AAUA.

‎Mai magana da yawun rundunar, DSP Olayinka Ayanlade, ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a ranar Asabar cewa ana zargin saurayin ɗalibar ne da kashe ta.

Advertisement

An Gano Wani Asibiti Da Ake Amfani Da Shi Wajen Sayar Da Jarirai

‎Ya bayyana cewa an kama mai gidan saurayin da wasu mutane da ake zargin sun taimaka wajen aikata kisan.

‎DSP Ayanlade, wanda bai bayyana sunan ɗalibar ba, ya ce ba’a kai ga kama saurayin da ake zargi da kisan ba.

Advertisement

‎NAN ta ruwaito cewa lamarin ya haddasa zanga-zangar lumana daga ɗaliban jami’ar a garin, inda suka tare hanyoyi da ababen hawa.

‎Sai dai mai magana da yawun rundunar ya ce ƴan sanda sun gana da masu zanga-zanga, kuma ankai ga dawo da zaman lafiya a yankin.

Advertisement

‎Da yake mayar da martani kan kisan, Shugaban Ƙungiyar Dalibai na AAUA, Mista Akeem Salami, ya yi Allah-wadai da yadda ake yawan kashe ɗaliban jami’ar ba gaira ba dalili.

‎Ya bayyana cewa bayan bincike an gano cewa an soka wa ɗalibar wuƙa har ta mutu, kuma aka bar gawarta a ɗakin saurayin fiye da kwanaki uku.

Advertisement

‎Shugaban SUG ɗin ya roƙi gwamnatin jihar, rundunar ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro da su ɗauki matakin daƙile irin wannan kisan gilla da ke faruwa akai-akai a cikin jami’ar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending