News
An Cafke Matasa 60 Bisa Zargin Ta’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi
An cafke matasa 60 da ake zargi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a wata gagarumar fafutukar da jami’an tsaro suka gudanar a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Babban jami’in da ke kula da shirin yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a jihar, Malam Sa’idu Jakusko, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis.
Wani Saurayi Yayi Ajalin Budurwarsa Da Ke Shekarar Karshe A Jami’a
Jakusko ya ce wannan samame ya gudana ne da haɗin gwiwar hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA da kuma wasu ƙungiyoyin sanya ido na cikin gida, inda aka cafke maza 30 da mata 30.
“Matakin ya zama wajibi, ganin yadda shaye-shaye ke ƙara zama ruwan dare a tsakanin matasa, musamman a cikin birane da wasu unguwanni da ke fama da matsalolin tsaro,” in ji shi.
Ya bayyana cewa, galibin wadanda aka cafke na taruwa ne a kusa da wani rafi da ke unguwar Gabari, inda ake zargin suna gudanar da harkar ta’ammali da ƙwayoyi.
Haka kuma, ya ce daga cikin wadanda aka kama akwai manyan dillalan miyagun ƙwayoyi guda uku da aka shafe lokaci ana farautarsu, kuma suna cikin jerin sunayen da jami’an tsaro ke nema ruwa a jallo.
Jakusko ya kara da cewa, za a ci gaba da tantance bayanan wadanda aka kama, kuma za a mayar da wadanda ba ‘yan jihar Yobe ba ne zuwa jihohinsu domin ci gaba da matakan shari’a da suka dace.
A yayin taron, wani fitaccen malamin addini, Sheikh Abubakar Muhammad, wanda aka gayyato domin yi wa wadanda ake zargi wa’azi da nasiha, ya shawarci matasan da su ji tsoron Allah tare da daina shiga hanyoyin da ke jefa su cikin halaka.
“Shekarunsu suna cikin lokacin da ya dace su gina rayuwarsu, amma abin takaici, sun rungumi halayen da ke lalata al’umma,” in ji Sheikh Abubakar.
Ya kuma yi kira ga iyaye da shugabannin al’umma da su taka rawar gani wajen kulawa da tarbiyyar matasa domin hana su fadawa tarkon miyagun dabi’u da ta’ammali da abubuwan da ke haifar da barna ga rayuwa da tsaro.
