News
Akalla Mutum 6 Sun Mutu Sanadiyyar Turmutsitsin Wurin Bauta A Indiya
Akalla mutum shida sun mutu a wani turmutsitsi da ya auku a wani shahararren wurin bauta na mabiya addinin Hindu a arewacin Indiya.
Hukumomin yankin sun sanar a ranar Lahadi cewa akwai mutane da dama da suka jikkata sakamakon fitar dango da masu neman tabarruki suka yi a wajen bautan a ranar Lahadi.
Lamarin ya faru ne a birnin Haridwar, inda ake yawan zuwa bauta bayan wani layin wutar lantarki mai karfin gaske ya fado a kan wata hanya kusa da wurin bautan.
Lamarin ya jefa masu ibada da dama cikin firgici inda mutane suka rika neman tsira da rayukansu.
Wani babban jami’in gwamnati a jihar Uttarakhand, Vinay Shankar Pandey ya tabbatar da mutuwar mutane shida, ya kuma ce masu ibadar sun fara guje-guje don tsira bayan faruwar lamarin.
Jami’an yankin sun ce dubban masu ibada ne suka taru a wajen da ke kan tsauni, wanda ya shahara wajen karbar bakuncin masu ibada na Hindu, musamman a karshen mako da kuma ranakun bukukuwa.
-
News23 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
