Connect with us

News

Hadarin Mota Ya Yi Ajalin Mutum 9 Yan Garin Dambatta A Hanyar Dawowa Daga Daurin Aure

Published

on

Mutane tara ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Katsina zuwa Kano.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 26 ga watan Yuli, 2025, kamar yadda wani mazaunin Dambatta a jihar Kano, Basiru Lawan, ya shaida  manema Labarai

Advertisement

Akalla Mutum 6  Sun Mutu Sanadiyyar Turmutsitsin Wurin Bauta A Indiya

Ya ce mutanen da abin ya rutsa da su dukkansu ‘yan karamar hukumar Dambatta ne, kuma sun dawo ne daga wani bikin aure da aka gudanar a jihar Katsina.

Hatsura a kan manyan titunan Najeriya na ci gaba da zama babban barazana ga rayuwar matafiya, inda aka ruwaito mutuwar fiye da mutane 14 kwanan nan a wani hadari da ya jawo gobara.

Advertisement

Haka kuma, watanni biyu da suka gabata, ‘yan wasa fiye da 20 daga jihar Kano sun mutu a wani hatsarin mota yayin da suke tafiya gasar ƙasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending