News
An Kama Wasu Sojoji Da Ake Zargi Da Shiga Ƙungiyar Asiri
Rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun ta ce ta kama wasu mutane da ake zargin sojoji ne, bisa tuhumar shiga cikin wata ƙungiyar asiri da ake zargi da haddasa rikice-rikice a jihar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Omolola Odutola, ya fitar ranar Lahadi, ya ce an cafke mutanen ne a wani samame da aka kai a Ijebu-Ode, bayan samun sahihan bayanan sirri daga wasu mazauna yankin.
Hadarin Mota Ya Yi Ajalin Mutum 9 Yan Garin Dambatta A Hanyar Dawowa Daga Daurin Aure
Odutola ya ce binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin na da alaƙa da ayyukan ƙungiyar asiri, kuma ana zargin suna amfani da matsayin su na soja wajen kare wasu da ake zargi da aikata laifuka.
“Sun dade suna ɗaukar nauyin tarukan ‘yan ƙungiyar, tare da kare wasu da ke aikata kisa da sauran laifuka masu tsanani,” in ji sanarwar.
Rundunar ‘yan sandan ta ce za a mika bayanan da suka tattara ga hukumomin soja domin gudanar da bincike da ɗaukar matakin da ya dace.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar ya ce za su ci gaba da kai farmaki kan ƙungiyoyin asiri da duk wanda aka samu da hannu a harkokinsu – komai matsayin sa.
-
News23 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
