Connect with us

News

Kwamaret Jaafar Abdullahi ya taya farfesa Sa’adatu murnar samun lambar yabo na cibiyar CBER a U.K

Published

on

img 1755504669228

DAGA JOHN D, WADA, A LAFIYA

Shugaban sashin labarai da jindadin ayuka wato Information and Protocol Unit a turance na babban jami’ar jihar Nasarawa (NSUK) dake birnin Keffi a jihar, kwamaret Jaafar Abdullahi Mohammed ya taya shugabar jami’ar, farfesa Sa’adatu Hassan Liman murnar samun wani lambar yabo na musamman wadda cibiyar nazarin kasuwanci da tattalin Arziki da akafi sani da (CBER) a takaice wadda ke U.K ta karrama ta a mako daya gabata.

Advertisement

Kwamaret Jaafar Abdullahi Mohammed yace tabbas karramawar da cibiyar nazarin kasuwanci da tattalin arzikin yayi wa farfesa Sa’adatu Hassan Liman ya cancanta bai kuma baiwa jami’ar da bangaren ilimin jihar baki daya mamaki ba idan akayi la’akari da nasarori da gagaruman gudumawa da take cigaba da bayar kafin da kuma zuwan ta a matsayin shugabar Jami’ar ta jihar.

2027: Usman Alhaji Ya Bukaci Matasa Su Yi Rijistar Katin Zaɓe Domain Zaɓar Shugabanni Nagari

Acewar Kwamaret Jaafar Abdullahi ba anan jihar Nasarawar kadai ba, farfesa Sa’adatu tana kuma yin duka mai yuwa anata bangaren a kuma kullun wajen tabbatar da ingancin harkokin ilimi a kasar nan ta Najeriya dama duniya baki daya da hakan nema ya jawo hankalin babbar cibiyar na kasar wajen ya karrama ta da lambar yabon na musamman.

Advertisement

Mai magana da yawun jami’ar ya kara da cewa bayan wannan, har ila yau kyautar ta kuma tabbatar da kyakkyawan jagorancin shugabar jami’ar ta NSUK, farfesa Sa’adatu Hassan Liman din ne da kuma kyakkyawan gudumawar da take bayarwa a fannin kasuwanci da tattalin arzikin jihar, Najeriya da duniya gabadaya.

Kwamaret Jaafar ya kuma yi amfani da damar inda ya jadda cewa taron mai taken: ROGE-Oxford 2025 wadda cibiyar ta CBER ta shirya ya hado masu ilimi, kwararru, masu tsara manufofi, da masu bincike daga kowanna bangaren duniya don tattaunawa kan muhimman batutuwa da suka shafi ci gaban kasuwanci da tattalin arzikin kasashen duniya baki daya inda ya kara da cewa

Advertisement

“karramawar da aka yi wa shugabar mu, farfesa Sa’adatu Hassan Liman a wannan taron tattalin arzikin duniya baki daya ya nuna himmatarta ne wajen bunkasa ilimi da inganta dorewa a tattalin arzikin duniya.

“Lalle ne, gabatarwar takardarta mai taken “Leadership Diversity, Equity and Inclusion (DEI) in organisational success: Perspectives from Leaders and Followers a turance” ya nuna kwarewarta da jagorancinta a fannin fiye da mitsali.

Advertisement

“Wannan nasarar ta kuma nuna himmatarta wajen jagorancin jami’a a fannin ilimi mai tsauyi, a duniya baki daya. muna anan muna taya ki murna wato farfesa Sa’adatu Hassan Liman kan wannan nasarar da ki ka yi fice,” in ji shi.

Cibiyar CBER cibiyar bincike ce ta kasuwanci da tattalin arziki na duniya baki daya wadda aka kafa a kasar London a shekarar 2006 da manufar bunkasa, karramawa da kuma tallafawa da kyau a fannin binciken kasuwanci da tattalin arziki kuma an karrama shugabar jami’ar NSUK din ce a wani wajen taro da aka gudanar a Said Business School a Jami’ar Oxford dake UK kenan a mako daya gabata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending