Connect with us

News

Gwamnati Kano Za Ta Ci Gaba Da Tallafawa Masu Taimaka Wa Shugabannin Kananan Hukumomi Kan Kafafen Sada Zumunta

Published

on

waiya 1365x2048 1

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta bayyana cewa za ta ci gaba da tallafawa mataimaka na musamman kan kafafen sada zumunta da ke aiki tare da shugabannin kananan hukumomin jihar guda 44.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karɓi bakuncin kungiyar mataimakan na musamman a ofishinsa.

Advertisement

Gwamnati Kano Za Ta Ci Gaba Da Tallafawa Masu Taimaka Wa Shugabannin Kananan Hukumomi Kan Kafafen Sada Zumunta

Waiya ya ce gwamnati na shirin ci gaba da basu goyon baya ta fannoni daban-daban, ciki har da shirya musu tarukan horo domin inganta ayyukansu. Ya ce, kamar yadda aka gudanar da wasu shirye-shirye a baya, gwamnati za ta ci gaba da amfani da kafafen sada zumunta wajen watsa manufofi da ayyukan gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa ga al’umma.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar mataimaka na musamman kan kafafen sada zumunta, ya bayyana cewa sun kai ziyara domin nuna godiya ga ƙoƙarin Kwamishinan wajen ganin cewa ayyukan gwamnatin Kano na isowa dukkan kananan hukumomi yadda ya kamata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending