Connect with us

News

An Sake Samun Kifewar Jirgin Ruwa Dauke Da Mutane A Sokoto

Published

on

kwale kwale

Akalla mutane shida sun rasa rayukansu yayin da wasu uku suka ɓace a wani hatsarin kwale-kwale a ƙauyen Garin Faji, ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto, a lokacin da mazauna yankin ke tserewa daga hare-haren ƴan bindiga.

Lamarin ya faru ne da safiyar Alhamis, 21 ga watan Agusta, kuma shi ne karo na biyu cikin mako guda, bayan wani hatsarin makamancin haka da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum huɗu a ƙaramar hukumar Goronyo.

Advertisement

Shalkwatar Tsaron Nijeriya Ta Yi Ƙarin Haske Kan Kalaman Da Babban Hafsan Tsaron Najeriya

Rahotanni daga mazauna yankin sun ce hare-haren ƴan bindiga da ke ci gaba da addabar yankin sun tilasta wa jama’a yin hijira ta hanyar koguna, lamarin da ya haifar da ƙarin hatsari da asarar rayuka.

Dan majalisar da ke wakiltar Sabon Birni ta Kudu, Hon. Aminu Boza, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce matsalar tsaro ta sa al’ummar yankin ke rayuwa cikin tsoro da barazana.

Advertisement

Gwamnatin jihar ta ce ta tura motocin yaƙi masu sulke don tallafawa jami’an tsaro a yankin. Sai dai akwai bukatar ƙarin matakan tsaro domin kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, SEMA, ta ce an ceto mutum 19 da ransu, yayin da ake ci gaba da neman waɗanda suka ɓace tare da haɗin gwiwar hukumar NEMA, NIWA, da Red Cross.

Advertisement

Hukumar ta ce hatsarin ya ƙara bayyana tsanantar matsalar tsaro a Sokoto, inda dubban jama’a ke ci gaba da rayuwa cikin tsoro da kaura daga gidajensu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending