Connect with us

News

Dakarun Sojin Najeriya Sun Ceto Mutane 76 Da Ƴanbindiga Suka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

Published

on

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 101 Sun Kama Wasu 182 A Cikin Mako Daya

Dakarun runudunar sojojin saman Najeriya sun kai hari maɓoyar ƙusurgumin ɗan bindigan nan Mustapha Babaro da ke jihar Katsina, inda suka samu nasarar ceto mutane 76 da aka yi garkuwa da su, ciki har da mata da ƙananan yara.

Rahotanni sun suna cewar sojojin sun kai farmakin ne a Tudun Pauwa na Ƙaramar Hukumar Kankara kuma an samu nasarar kuɓutar da dukkan mutanen da aka sace a lokacin harin da aka kai Unguwar Gidan Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a makon da ya gabata, duk da dai an samu mutuwar yaro ɗaya.

Advertisement

An Sake Samun Kifewar Jirgin Ruwa Dauke Da Mutane A Sokoto

Bayaga wannan nasara, haka nan rundunar sojojin saman Najeriya ta kuma samu nasarar kashe masu tada kayar baya 35, a lokacin da suke ƙoƙarin kai hari a iyakokin ƙasar da Kamaru.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

FRI HAUSA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending