Connect with us

News

Gidauniyar AMG Ta Fara Shirye-shiryen Samar Da Asusun Agajin Gaggawa A Kano

Published

on

IMG 20250825 WA0002

DAGA SAFIYA MUHAMMAD

Gidauniyar Dr. Magashi Garba (AMG Foundation) tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Jinƙai ta Jihar Kano ta gudanar da taron kwana ɗaya domin tattauna hanyoyin samar da Asusun Agajin Gaggawa don ƙara inganta harkokin lafiya da ilimi ga al’ummar jihar.

Advertisement

Shugaban gidauniyar, Dr. Aminu Magashi Garba, ya bayyana cewa taron ya zo ne a daidai lokacin da ake buƙatar sabon tsarin tallafa wa al’umma, musamman wajen magance matsalolin kiwon lafiya da karatun ‘ya’yan ƙasa.

Dakarun Sojin Najeriya Sun Ceto Mutane 76 Da Ƴanbindiga Suka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

“Lafiya da ilimi su ne ginshiƙan ci gaban kowace al’umma. Saboda haka akwai buƙatar gwamnati ta ɗauki ƙarin matakai na musamman don samar da asusun da zai taimaka wajen ceto rayuka da bunƙasa fannin ilimi a Kano baki ɗaya,” in ji Dr. Magashi.

Advertisement

Shi ma Kwamishinan Ma’aikatar Jinƙai ta Jihar Kano, Hon. Adamu Aliyu Kibiya, ya jaddada buƙatar haɗin kai tsakanin gwamnati, kungiyoyin farar hula, da masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da ci gaban jihar.

“Idan aka samar da wannan asusu, zai taka muhimmiyar rawa wajen rage raɗaɗi da matsalolin da jama’a ke fuskanta,” a cewar Kibiya.

Advertisement

A cewar wakiliyar mu, Safiya Muhammad Usman, mahalarta taron sun yi kira ga gwamnatin tarayya, ta jiha, da ‘yan kasuwa da su haɗa hannu don samar da asusun agajin gaggawa, domin kare rayukan al’umma a lokutan haɗari da matsalolin lafiya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending