Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Ware N7.5bn Ga Hukumar Ruwa Amma Ta Kashe N1.5m Kacal A Watanni Shida

Published

on

water crisis is a serious threats in India and worldwide

Duk da matsanancin ƙarancin ruwa da ake fama da shi a Kano, gwamnatin jihar ta kasa aiwatar da kasafin kuɗi yadda ya kamata a fannin samar da ruwan sha.

Rahoton tantancewar kasafin kuɗin rabin shekara ta farko ta 2025, wanda jaridar SolaceBase ta bibiya, ya nuna cewa cikin Naira biliyan 7.5 da aka ware wa Hukumar Ruwa ta Kano, an kashe Naira miliyan 1.5 kacal a cikin watanni shida na farko na shekarar. Wannan na nufin cewa kashi 0.0% kacal na kuɗaɗen da aka tanada aka aiwatar.

Advertisement

Kyautar N200,000 Ga Dalibar Da Ta Lashe Gasar Duniya Ta Fallasa Darajar Ilimi A Najeriya

Rahoton ya bayyana cewa matsalar ta fi tsananta a kananan hukumomin Dala, Fagge, Gwale, Kano Municipal, Kumbotso, Tarauni, Nassarawa da Ungogo, inda jama’a ke dogaro da rijiyoyin burtsatse da masu sayar da ruwa domin samun ruwan sha da na amfani a kullum.

A shekarar 2024, gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan 8.5 domin fannin ruwa amma ta kashe Naira biliyan 1.08 kacal, wanda ya kai kashi 12.6% kacal na kasafin.

Advertisement

Bugu da ƙari, rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) mai taken Multidimensional Poverty Index ya nuna cewa kaso 31% na iyalai a Kano ba su da ruwan sha mai tsafta. Wannan na ƙara tabbatar da matsalar samar da ruwa mai inganci a jihar.

Hukumar Ruwa ta Kano dai tana daga cikin muhimman sassan gwamnati da ke da alhakin samar da ruwa ga al’umma, musamman a birane da wasu manyan ƙananan hukumomi. Duk da haka, adadin kuɗin da ake kashewa a wannan bangare ya ci gaba da jawo tambayoyi daga masana harkar tattalin arziki da al’

Advertisement

ummar jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending