News
Matsalar Ruwan Sha: Matan Aure Da ’Yan Mata Na Kwana Waje Don Neman Ruwa A Kauyukan Kano
Matan aure da ’yan mata a wasu kauyuka na Jihar Kano na kwana a wajen rijiyoyi da fanfunan ruwa saboda ƙarancin ruwan sha da ya addabi yankin.
A kauyen Yar Manman, da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa, al’umma na fama da matsalar ruwan sha da ta kai ga mata da yara na kwana a wajen kalolin ruwa, su na jiran layi ko jiran ruwan ya cika.
Kotu Ta Tura Matasa Gidan Yari Kan Yunkurin Hana Zance A Kano
A cewar mazauna yankin, shekaru sama da 25 ke nan da su ke fama da wannan matsala ba tare da an samu mafita daga gwamnati ba.
“Wannan ruwan da muke sha, dabbobi da mutane ne ke haduwa a wajen. Amma ba mu da wani zaɓi, sai mu sha shi ko da kuwa yana da haɗari,” inji wata mata da ke zaune a kauyen Yar Manman.
Fiye da mutane 10,000 daga kauyen da kuma wasu ƙauyuka biyar da ke kusa da shi ne ke amfani da ruwan.
A yanzu haka, wasu yara mata sun daina zuwa makaranta saboda sai sun fita neman ruwa tun da asuba, kuma su na dawowa da yamma su gaji, har ba su iya komai.
“Yanzu yara mata basa zuwa makaranta, su na ta fita neman ruwa. Ko sun dawo gajiya ce kawai,” inji wani mazaunin kauyen.
Wannan matsala na haddasa yaduwar cututtuka masu nasaba da rashin tsaftar ruwa, kamar amai da gudawa da ciwon ciki, lamarin da ke barazana ga lafiyar jama’a.
MATASHIYA TV ta ruwaito cewa masu ruwa da tsaki a yankin na roƙon gwamnatin jiha da ta tarayya da kuma kungiyoyin agaji su shigo cikin lamarin da gaggawa, domin samar da rijiyoyi ko bututun ruwa da zai taimaka wa al’umma wajen samun ruwan sha mai tsafta.
