Connect with us

News

Jami’an Ƴan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ya Kashe Ƙaninsa Ya Ɓoye Gawar A Cikin Duro

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Hukumar Ƴan Sandan Jihar Ondo ta kama wani mutum mai suna Eze Elechi Amadi bisa zargin kashe ƙaninsa, Otu Ifeanyi mai shekara 18, sannan ya yi ƙoƙarin ɓoye gawar sa a cikin duro.

Lamarin ya faru ne a unguwar Kajola da ke Ƙaramar Hukumar Odigbo, inda wanda ake zargin ya bayyana cewa rikicin kuɗi tsakaninsa da ƙaninsa ne ya jawo kisan.

Advertisement

Jami’an Hisba Sun Kama Matasa Da Shigar Da Ta Sabawa Addini Da Ta Dodanni A Zagayen Takutaha

Kwamishinan Ƴan Sanda na jihar, Adebowale Lawal, ya bayyana cewa a ranar 26 ga watan Agusta, 2025, da misalin ƙarfe 3:00 na rana, wani mazaunin Kajola mai suna Oluwafemi Oladipupo ya kai rahoto a ofishin ƴan sanda bayan ya ga wani duro na roba mai launin shuɗi a gaban gidansa, wanda aka ɗaure bakinsa da igiya baƙa.

A cewarsa, bayan jami’an tsaro sun buɗe duro ɗin, sai aka gano gawar matashin mai suna Otu Ifeanyi, daga bisani kuma aka tabbatar shi ne ƙaninsa na jini.

Advertisement

“An kama wanda ake zargin yayin da yake ƙoƙarin jefar da duro ɗin a wani wurin da ba a sani ba, bayan ya zame daga babur ɗin da yake tuƙawa. Yayin bincike, ya amsa cewa shi ne ya kashe ƙaninsa saboda rikicin kuɗi, inda ya ce marigayin ya kwashe masa Naira 20,000 daga asusun Ecobank ɗinsa ba tare da yardarsa ba,” in ji Lawal.

Kwamishinan ya ƙara da cewa gawar an ajiye ta a ɗakin ajiye gawa yayin da bincike ke ci gaba, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

Advertisement

An kama mutum 99 bisa zargin laifuka daban-daban

Bugu da ƙari, Lawal ya bayyana cewa rundunar ƴan sandan jihar ta kama mutum 99 a faɗin ƙananan hukumomi 18 bisa zargin aikata manyan laifuka da suka haɗa da kisan kai, garkuwa da mutane, fashi da makami, shiga ƙungiyoyin asiri, safarar miyagun ƙwayoyi, da sata.

Advertisement

A cewarsa, “Waɗannan nasarori ba wai kawai sun nuna jajircewar jami’anmu ba, har ma sun fito da muhimmancin haɗin kai daga al’ummar jihar, waɗanda suka bayar da bayanai da suka taimaka wajen kama masuaikata laifuka.”

 

Advertisement

LEADSHIP

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending