Connect with us

News

‎Akalla Mutane Hudu Ne Suka Rasu Bayan Da Hilux Ta Yi Karo Da Tankar Gas A Kaduna

Published

on

Accident

Akalla mutane hudu ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru da yammacin Lahadi a kan babban titin Kaduna–Abuja, kusa da Kakau, Gonin Gora, a jihar Kaduna.

‎Hukumar Kiyaye Hadura ta Ƙasa (FRSC), reshen jihar Kaduna, ta tabbatar da faruwar hatsarin. Kwamandan FRSC na jihar, Iliyasu Tijjani, ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, lokacin da motar Hilux mai saurin gaske ta yi karo da tankar gas.

Advertisement

Mutuwar Tsohon Sojan Nijeriya Ta Tilasta Jirgin British Airways Saukar Gaggawa A Barcelona

‎ “Binciken farko ya nuna cewa gudu fiye da ƙa’ida da gangancin wucewa sune manyan abubuwan da suka haddasa hatsarin,” in ji Tijjani.

‎A cewar FRSC, mutane biyar ne ke cikin motar Hilux – maza hudu da mace ɗaya. Duk maza hudu sun mutu a Asibitin St. Gerard Catholic, yayin da mace ɗaya ke samun kulawa a Asibitin FRSC, Tollgate, Kaduna.

Advertisement

‎Karo ya lalata motar Hilux sosai, sannan ya janyo cunkoson ababen hawa na ɗan lokaci kafin jami’an ceto su isa wurin.

‎Kwamandan ya yi kira ga direbobi da su guji gudu fiye da ƙa’ida da gangancin wucewa, yana mai jaddada cewa mafi yawan hatsarurrukan da ke faruwa a titin Kaduna–Abuja na faruwa ne saboda rashin haƙuri da take dokokin zirga-zirga.

Advertisement

 

Advertisement

PM NEWS 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending