Connect with us

News

Mutuwar Tsohon Sojan Nijeriya Ta Tilasta Jirgin British Airways Saukar Gaggawa A Barcelona

Published

on

British Aurways Diverts

Wani jirgin kamfanin British Airways da ya taso daga Landan zuwa Abuja ya yi saukar gaggawa a birnin Barcelona na ƙasar Sifaniya bayan da wani tsohon sojan sama na Najeriya ya rasu a cikin jirgin yayin tafiya.

Lamarin ya faru ne a safiyar Litinin bayan jirgin ya bar filin jirgin sama na Heathrow da misalin ƙarfe 11:00 na dare a jiya Lahadi, da nufin sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin ƙarfe 5:00 na safiyar yau.

Advertisement

An Kama Wani Da Ake Zargi Da Kashe Matarsa Da Gatari Bayan Bikin Haihuwar Ɗansu

Sai dai a cewar majiyoyi, tsohon sojan, wanda ya fito daga jihar Anambra, ya rasu ne a cikin jirgin da misalin ƙarfe 1:30 na dare, lamarin da ya tilasta wa matuƙan jirgin sauka gaggawa a filin jirgin sama na El Prat da ke Barcelona domin gudanar da matakan gaggawa.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin, wanda ke da shekaru fiye da 80, ya dade yana fama da rashin lafiya kafin rasuwarsa. An kuma ce yana daga cikin tsoffin sojojin sama da suka yi ritaya daga jihar Anambra da har yanzu suke raye kafin wannan lokaci.

Advertisement

Rasuwarsa ta jefa iyalansa da abokan aikinsa tsoffin sojoji cikin jimami da alhini, yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin iyalansa da hukumomin jirgin kan matakan gaba.

 

Advertisement

 

BLUEPRINT

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending