Connect with us

News

‎Majalisar Masarautar Kano Ta Taya Maude Murnar Samun Mukamin SAN Da Nadin Kwamishinan Shari’a

Published

on

IMG 20251015 WA0002

Majalisar Masarautar Kano ta taya Babban Lauyan Jihar Kano, Abdulkarim Kabiru Maude, murnar samun lambar yabo ta Senior Advocate of Nigeria (SAN), da kuma nadinsa a matsayin Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Jihar Kano.

A wata sanarwa da mai taimaka wa kwamishinan a fannin yada labarai, Abubakar Tijjani Ibrahim, ya fitar, ta ce tawagar majalisar ƙarƙashin jagorancin Alhaji Aliyu Ibrahim Ahmed, Matawallen Kano, ta kai ziyara ofishin Maude da ke Sakatariyar Audu Bako a ranar Talata domin mika wasikar taya murna a madadin Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II (PhD, CON).

Advertisement

Kwamishinan Shari’a na Kano Ya Jagoranci Taron Farko Don Inganta Ayyukan Shari’a

Majalisar ta ce wannan karramawa da nadin mukami biyu da Maude ya samu, na nuna irin jajircewarsa, gaskiyarsa da sadaukarwarsa wajen tabbatar da adalci da inganta mulkin doka a Kano da Najeriya baki ɗaya.

“Tare da ilimi, kwarewa da hangen nesa da Allah Ya ba ka, muna da tabbacin cewa za ka gudanar da aikinka cikin kwarewa, kuma za ka taka muhimmiyar rawa wajen inganta shari’a da ci gaban Kano,” in ji majalisar.

Advertisement

Da yake mayar da martani, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya gode wa Mai Martaba Sarkin Kano da majalisar masarautar bisa wannan girmamawa, yana mai cewa wannan yabo ya ƙara masa ƙaimi da kwarin gwiwa wajen ci gaba da aikin tabbatar da adalci da gaskiya a jihar.

“Addu’o’in Mai Martaba da majalisar suna da matuƙar muhimmanci a gare ni. Zan ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da adalci da gaskiya a Kano,” in ji shi.

Advertisement

Ziyarar ta ƙare da addu’o’i na neman nasara ga kwamishinan da kuma zaman lafiya da ci gaba ga jihar Kano baki ɗaya.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending