News
Kwamishinan Shari’a na Kano Ya Jagoranci Taron Farko Don Inganta Ayyukan Shari’a
Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma Babban Lauyan Gwamnati, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya jagoranci taron farko na Kano State Justice Sector Reform Team, domin ƙarfafa tsarin shari’a da tabbatar da adalci a fadin jihar.
Taron, wanda aka gudanar a ofishin Ma’aikatar Shari’a da ke Kano, ya samu halartar Solicitor-General na Jihar Kano, Barr. Salisu Tahir, shugabannin sassa daban-daban, da Co-chairperson na tawagar, Hajiya Fatima Kwaku.
An kafa tawagar gyaran tsarin shari’a tun a shekarar 2013, bisa dokar Justice Sector Reform Law, domin gyara tsarin shari’a ta hanyar ƙarfafa sulhu kafin kai ƙara kotu, rage take hakkin bil’adama, da sauƙaƙa wa jama’a samun kariya da shawarar lauya.
A jawabin sa, Barrister Maude ya bayyana cewa gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na da kudurin tallafawa ayyukan tawagar, domin tabbatar da gaskiya da inganci a tsarin shari’a, yana mai cewa tsarin shari’a shi ne ginshiƙin zaman lafiya da ci gaban jihar.
Co-chairperson Hajiya Fatima Kwaku ta nuna farin cikinta da nadin Barrister Maude a matsayin shugaban tawagar, tana mai cewa jagorancinsa zai kawo sauyi mai ma’ana ga tsarin shari’a a Kano, inda ta ce hangen nesansa da jajircewarsa wajen haɗa kai da kowa zai kawo sabuwar fata ga al’umma.
Daga cikin mahalarta taron akwai Hajiya Sakina Datti, Daraktar kare haƙƙin jama’a; Hajiya Hafsat Wali, Daraktar shari’ar Musulunci; Malam Ibrahim Bello, Ko’odineta na Rule of Law and Anti-Corruption (RoLAC); da Hajiya Hajara Garba Ahmed, Babbar Sakatare a Babbar Kotun Kano.
