News
Kano: Tsohon Ma’aikacin Gwamnati Da Ya Sadaukar Kudin Fanshonsa Domin Gina Masallacin Juma’a Ya Rasu Yana Da Shekara 96
Wani Tsohon ma’aikacin gwamnati mai ritaya, Alhaji Bello Abdullahi (Sarkin Shangu Murabus), wanda ya bayar da dukkanin kudin fanshonsa na kimanin Naira miliyan biyar domin gina Masallacin Juma’a a garin Shangu da ke Ƙaramar Hukumar Rano a Jihar Kano, ya rasu yana da shekaru 96 a Duniya.
Rahotanni sun ce Alhaji Bello ya rasu ne bayan fama da jinya na tsawon lokaci, lamarin da ya sanya al’ummomin Rano da Kibiya cikin jimami.
Marigayi Alhaji Bello tsohon ma’aikacin gwamnati ne da aka san shi da tawali’u, tsananin bin addini da taimakon jama’a, inda jama’a ke kallonsa a matsayin mutum mai kishin al’umma.
Ya bar mata uku, ’ya’ya 26, da jikoki sama da 100. Daga cikin ’ya’yansa akwai Alhaji Akilu Bello, Kwamandan Hukumar Shige da Fice (Immigration) na Yankin Bauchi, da kuma Hajiya Gadaru Bello, matar tsohon Babban Kwamandan Hukumar Shige da Fice ta ƙasa, Alhaji Baba Dede.
Tun kafin rasuwarsa, Alhaji Bello ya dauki mataki da ya jawo hankalin jama’a bayan yanke shawarar bayar da dukkanin kudin fanshonsa domin tallafa wa aikin gina Masallacin Juma’a na tsakiyar garin Shangu.
Ɗansa, Alhaji Abdullahi Bello, Sarkin Garin Shangu, ya bayyana cewa an tsara masallacin ne domin ya zama cibiyar ibada da koyar da ilimin addinin Musulunci,
Masallacin Juma’ar Shangu na ci gaba da kasancewa abin tunawa ga rayuwar Alhaji Bello Abdullahi, wanda jama’a ke bayyana a matsayin mutum mai imani da sadaukarwa ga al’umma.
